2 Korintiyawa 11:22-33
22
In su Ibraniyawa ne, ni ma haka. In su Isra’ilawa ne, ni ma haka. In su zuriyar Ibrahim ne, ni ma haka.
23
In su bayin Kiristi ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! Ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan dauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri-iri.
24
Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu.
25
Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni.
26
Na yi tafiye-tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin ’yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin ’yan’uwa na ƙarya.
27
Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara.
28
Ban da waɗannan abubuwa, kowace rana ina ɗauke da nauyin kula da dukan ikkilisiyoyi.
29
Wane ne ya rasa ƙarfi, da ban ji shi a jikina ba? Wane ne ya fāɗi cikin zunubi, da ban ji zafin wannan ba?
30
In ma lalle ne in yi taƙama, to, sai in yi taƙama da abubuwan da suka nuna rashin ƙarfina.
31
Allah Uban Ubangiji Yesu Kiristi, wanda yabo ta tabbata a gare shi har abada, ya san cewa ba ƙarya nake yi ba.
32
A Damaskus, gwamnan da yake ƙarƙashin Sarki Aretas, ya sa tsare ƙofofin birnin Damaskus, don yă kama ni.
33
Amma aka saukar da ni cikin kwando ta tagar katanga, na kuɓuce masa.
Settings