1 Sama’ila 9:15-24
15
Kafin zuwa Shawulu, Ubangiji ya riga ya bayyana wa Sama’ila ya ce,
16
“Gobe war haka zan aiko maka da wani mutum daga ƙasar Benyamin. Ka keɓe shi shugaban mutanena Isra’ila. Shi zai cece mutanena daga hannun Filistiyawa. Na ga azabar mutanena gama kukansu ya hauro wurina.”
17
Da Sama’ila ya hangi Shawulu, Ubangiji ya ce masa, “Ga mutumin da na yi maka magana, shi ne zai bi da mutanena.”
18
Shawulu ya sami Sama’ila a hanyar shiga gari, sai ya tambaye shi ya ce, “Ina roƙonka ka nuna mini gidan mai duba?”
19
Sama’ila ya ce, “Ni ne mai duban, ka yi gaba zuwa ka tudu, gama yau za ka ci tare da ni, da safe kuma in sallame ka, in gaya muku duk abin da yake a zuciyarku.
20
Game da jakunan da suka ɓace kwana uku kuwa, kada ka damu, an same su. Ga wane ne Isra’ila ta sa dukan zuciya, in ba ga kai da kuma dukan iyalin mahaifinka ba?”
21
Shawulu ya ce, “Ashe, ni ba mutumin Benyamin ba ne daga ƙaramar kabila ta Isra’ila? Dangina kuma ba shi ba ne mafi kakanni a cikin kabilar Benyamin ba? Yaya za ka faɗa mini irin wannan magana.”
22
Sa’an nan Sama’ila ya shiga da Shawulu da baransa ya zaunar da su a gaban waɗanda aka gayyata, mutanen sun kai wajen mutum talatin.
23
Sama’ila ya ce wa mai dahuwa, “Kawo naman da na ba ka, wannan da na ce ka ajiye dabam.”
24
Sai mai dahuwan ya ɗauko cinya da abin da yake bisanta ya kawo ya ajiye a gaban Shawulu. Sama’ila ya ce, “Ga abin da aka ajiye dominka. Ka ci, gama an keɓe shi dominka saboda wannan hidima daga lokacin da na ce, ‘Na gayyaci baƙi.’ ” Shawulu kuwa ya ci tare da Sama’ila a ranan nan.
Settings