Skip to content
1 Sama’ila 17:45-58

1 Sama’ila 17:45-58

45
Dawuda ya ce wa Bafilistin, “Kana zuwa ka yaƙe ni da māshi da takobi da kere, amma ni ina zuwa in yaƙe ka a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki, Allah na rundunar Isra’ila, wanda ka rena.
46
Yau nan, Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan kuwa kashe ka, in datse kanka. Yau, zan ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namun jeji, da haka duniya za tă sani lalle akwai Allah a cikin Isra’ila.
47
Duk waɗanda suka taru a nan za su san cewa ba da māshi ko takobi ne Ubangiji yake ceto ba, gama yaƙin nan na Ubangiji ne, shi kuwa zai bashe ku duka a hannuwanmu.”
48
Yayinda Bafilistin yana matsowa kusa domin yă fāɗa wa Dawuda, sai Dawuda ya ruga a guje zuwa bakin dāgā don yă same shi.
49
Ya sa hannu a jakarsa ya ɗauki dutse, ya sa cikin majajjawa ya wurga, dutsen kuwa ya bugi Bafilistin a goshi, dutsen ya shiga cikin goshinsa, sai Bafilistin ya fāɗi rubda ciki.
50
Da majajjawa da dutse kawai Dawuda ya ci nasara a kan Bafilistin. Ya buge shi, ya kashe shi ba tare da takobi a hannunsa ba.
51
Dawuda ya ruga ya tsaya a bisan Bafilistin, ya zare takobin Bafilistin daga kubensa, ya datse masa kai da shi. Da Filistiyawa suka ga jaruminsu ya mutu, sai suka juya suka gudu.
52
Mutanen Isra’ila da na Yahuda suka rugo gaba da babbar murya, suka fafari Filistiyawa har zuwa mashigin Gat da kuma ƙofofin Ekron. Gawawwakin Filistiyawa suka bazu a hanyar Sha’arayim zuwa Gat da kuma Ekron.
53
Da Isra’ilawa suka komo daga bin Filistiyawa sai suka washe sansanin Filistiyawa.
54
Dawuda ya ɗauki kan Bafilistin zuwa Urushalima. Sai Dawuda ya ajiye kayan yaƙin Bafilistin a tentinsa.
55
Yayinda Shawulu yake kallon Dawuda sa’ad da za shi yă yaƙi Bafilistin, sai ya tambayi Abner, komandan rundunarsa ya ce, “Abner, ɗan wane ne wannan saurayi?” Abner ya ce ran sarki yă daɗe, “Ban sani ba.”
56
Sarki ya ce, “Ka tambaya mini ko yaron wane ne wannan saurayi.”
57
Dawuda yana dawowa daga karkashe Filistiyawa ke nan, sai Abner ya kai shi gaban Shawulu, riƙe da kan Bafilistin.
58
Sai Shawulu ya ce, “Kai ɗan wane ne, saurayi?” Dawuda ya ce, “Ni ɗan bawanka Yesse ne, na Betlehem.”

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options