1 Sama’ila 15:1-23
1
Sama’ila ya ce wa Shawulu, “Ni ne wanda Ubangiji ya aika in shafe ka ka zama sarki bisa mutanensa Isra’ila. Saurara yanzu ka ji saƙo daga wurin Ubangiji.
2
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Zan hori Amalekawa saboda abin da suka yi wa Isra’ila sa’ad da suka ba su wahala yayinda suka fito daga Masar.
3
Yanzu ka tafi ka yaƙi Amalekawa, ka hallaka kome da yake nasu, kada ka bar su da rai, ka kashe maza, da mata, da yara, da jarirai, da dabbobi, da tumaki, da raƙuma, da kuma jakuna.’ ”
4
Sai Shawulu ya tattara sojoji, ya ƙidaya su a Telayim, ya sami su dubu ɗari biyu da dubu goma daga Yahuda.
5
Shawulu ya tafi birnin Amalek ya yi kwanto a kwari.
6
Sai Shawulu ya ce wa Keniyawa, “Ku tashi ku bar Amalekawa don kada in hallaka ku tare da su, saboda kun yi wa dukan Isra’ilawa kirki, lokacin da suka fito daga Masar.” Saboda haka Keniyawa suka tashi suka bar Amalekawa.
7
Sa’an nan Shawulu ya ci Amalekawa da yaƙi tun daga Hawila har zuwa Shur, a gabashin iyakar Masar.
8
Ya kama Agag sarkin Amalekawa da rai. Ya kuma hallaka dukan mutanensa da takobi.
9
Amma Shawulu da sojojinsa suka bar Agag, da tumaki, da shanu, da ’yan maruƙa masu ƙiba da kuma duk abin da yake mai kyau da rai. Waɗannan ba su so su hallaka su gaba ɗaya ba, amma duk abin da ba a so da kuma marar amfani suka hallaka.
10
Sai Ubangiji ya yi magana da Sama’ila ya ce,
11
“Na damu da na naɗa Shawulu sarki, domin ya juya mini baya, bai kuma bi umarnina ba.” Sama’ila ya damu ƙwarai, ya yi kuka ga Ubangiji dukan dare.
12
Kashegari da sassafe sai Sama’ila ya tashi ya tafi domin yă sadu da Shawulu, amma aka gaya masa cewa Shawulu ya tafi Karmel. A can ya yi wa kansa abin tunawa don yă girmama kansa, daga can kuma ya juya ya gangara zuwa Gilgal.
13
Da Sama’ila ya kai wurinsa, sai Shawulu ya ce, “Ubangiji yă albarkace ka, na aikata umarnin Ubangiji.”
14
Amma Sama’ila ya ce, “Ashe, waɗannan ba kukan tumaki ke nan nake ji a kunnena ba? Wane kuka shanu ke nan nake ji?”
15
Shawulu ya amsa ya ce, “Sojoji ne suka kawo su daga Amalekawa. Sun bar tumaki da shanu masu kyau da rai don su yi wa Ubangiji Allahnka hadaya, amma sauran mun hallaka duka.”
16
Sama’ila ya ce, “Dakata, bari in faɗa maka abin da Ubangiji ya ce mini jiya da dare.” Shawulu ya ce, “Gaya mini.”
17
Sama’ila ya ce, “Ko da yake kana ganin kanka kai ba wani abu ne ba, ashe, ba kai ne yanzu shugaban kabilan Isra’ila ba? Ubangiji ya shafe ka ka zama sarkin Isra’ila.
18
Shi kuma ya aika, ya umarce ka cewa, ‘Tafi ka hallaka Amalekawa mugayen mutanen nan duka, ka yaƙe su sai ka share su ƙaf.’
19
Me ya sa ba ka bi umarnin Ubangiji ba? Me ya sa ka sa hannu a ganima, ka kuma yi mugun abu a gaban Ubangiji?”
20
Shawulu ya ce, “Amma na bi umarnin Ubangiji. Na bi saƙon da Ubangiji ya ba ni. Na hallaka Amalekawa, na kuma kamo Agag sarkinsu.
21
Sojoji suka kawo tumaki da shanu mafi kyau daga cikin ganimar domin a miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnka a Gilgal.”
22
Amma Sama’ila ya ce, “Ubangiji yana murna da sadaka da hadaya fiye da biyayya ga maganar Ubangiji? Yin biyayya ta fi hadaya a kula kuma ta fi ƙibabbun raguna.
23
Gama tawaye yana kama da zunubi na duba, girman kai kuma yana kama da bautar gumaka. Saboda ka ƙi maganar Ubangiji, shi ma ya ƙi ka da zaman sarki.”
Settings