1 Sarakuna 2:1-9
1
Da lokacin mutuwar Dawuda ya yi kusa, sai ya gargaɗe Solomon ɗansa, ya ce,
2
“Ina gab da bin hanyar da kowa a duniya zai bi. Saboda haka ka yi ƙarfin hali, ka nuna kanka namiji,
3
ka kiyaye abin da Ubangiji Allahnka yake bukata. Yi tafiya a hanyoyinsa, ka kiyaye ƙa’idodi, da umarnai, da dokoki, da kuma farillansa, kamar yadda suke a rubuce a Dokar Musa, don ka yi nasara a cikin kome da za ka yi, da kuma inda za ka tafi.
4
Ubangiji kuwa zai kiyaye alkawarinsa gare ni da ya ce, ‘In zuriyarka suka lura da yadda suke rayuwa, in kuma suka yi tafiya da aminci a gabana da dukan zuciyarsu, da kuma dukan ransu, ba za ka kāsa samun mutum a kujerar sarautar Isra’ila ba.’
5
“Yanzu fa, kai kanka ka san abin da Yowab ɗan Zeruhiya ya yi mini. Abin da ya yi wa shugabanni biyun nan na mayaƙan Isra’ila, wato, Abner ɗan Ner, da Amasa ɗan Yeter. Ya kashe su, ya kuma zub da jininsu a lokacin salama sai ka ce a fage yaƙi, da wannan jini ya yi ɗamara a gindinsa, ya kuma sa takalma a ƙafafunsa.
6
Ka yi da shi gwargwadon hikimarka, amma kada ka bari yă gangara kabari da furfura cikin salama.
7
“Amma ka yi alheri ga ’ya’yan Barzillai mutumin Gileyad, ka sa su kasance a cikin waɗanda suke ci a teburinka. Sun goyi bayana sa’ad da nake gudu daga ɗan’uwanka Absalom.
8
“Ka tuna, akwai kuma Shimeyi ɗan Gera, mutumin Benyamin daga Bahurim, wanda ya yi ta yin mini muguwar la’ana a ranar da na tafi Mahanayim. Sa’ad da ya gangara ya same ni a Urdun, na rantse masa da sunan Ubangiji na ce, ‘Ba zan kashe ka da takobi ba.’
9
Amma yanzu, kada ka ɗauke shi marar laifi. Kai mutum ne mai hikima; za ka san abin da za ka yi da shi. Ka kawo furfuransa zuwa kabari da jini.”
Settings