1 Korintiyawa 14:6-25
6
To, ’yan’uwa, a ce na zo wurinku ina kuma yin magana da waɗansu harsuna, amfanin me zan yi muku in ban zo muku da wani bayani ko sani ko annabci, ko kuma kalmar koyarwa ba?
7
Abubuwan nan marasa rai ma da sukan yi ƙara, kamar su algaita ko molo, in muryarsu ba tă fita sosai ba, yaya wani zai san abin da ake busawa ko kaɗawa?
8
Haka ma in ba a busa ƙaho sosai ba, wa zai yi shirin yaƙi?
9
Haka yake sa’ad da kuka yi magana da waɗansu harsunan da ba a fahimta. In babu wanda zai san abin da kuke faɗi, za ka dai yi wa iska magana ne kawai.
10
Ba shakka akwai harsuna iri-iri a duniya, duk da haka kowane a cikinsu yana da ma’ana.
11
To, in ban gane ma’anar abin da wani yake faɗi ba, ni baƙo ne ga mai maganar, shi kuma baƙo ne a gare ni.
12
Haka yake a gare ku. Da yake kuna marmarin samun baye-bayen ruhaniya, sai ku ba da ƙarfinku ga yin amfani da waɗanda za su gina ikkilisiya.
13
Saboda haka, duk wanda yake magana da harshe, sai yă yi addu’a a yi masa baiwar fassara.
14
Gama in na yi addu’a da wani harshe, ruhuna ne yake addu’a, amma tunanina bai amfana kome ba.
15
To, me zan yi? Akwai lokutan da zan yi addu’a da ruhuna; akwai kuma lokutan da zan yi addu’a da hankalina. Wani lokaci ya kamata in yi waƙa da ruhuna, a wani lokacin kuma in yi waƙa da hankalina.
16
A cewa waɗansu baƙi suna cikin sujadarku, sa’ad da kuke yabon Allah da ruhunku, yaya waɗanda suke tare ku za su fahimta, har su ce, “Amin,” da yake ba su san abin da kuke faɗi ba?
17
Ko da yake kuna ba da godiya da kyau, amma wancan mutumin da yake tare da ku bai ginu ba.
18
Na gode wa Allah, domin ina magana da harsuna fiye da ku duka.
19
Amma a cikin ikkilisiya zan gwammace in yi magana da kalmomi biyar da za a fahimta don in koyar da waɗansu da a ce in yi magana da kalmomi guda dubu goma a wani harshe.
20
’Yan’uwa, ku daina tunani kamar yara. Wajen mugunta ku zama jarirai, sai dai wajen tunaninku, ku zama manya.
21
A cikin Doka yana a rubuce cewa, “Ta wurin mutane masu baƙin harsuna da kuma ta leɓunan baƙi zan yi magana da waɗannan mutane, amma duk da haka, ba za su saurare ni ba,” in ji Ubangiji.
22
Harsuna fa alama ce ba ga masu bi ba, sai dai ga marasa bi. Annabci kuwa ga masu bi ne ba ga marasa bi ba.
23
Saboda haka, in dukan ikkilisiya ta taru, kowa kuma yana magana da waɗansu harsuna, sai waɗansu jahilai ko waɗansu marasa bi suka shigo, ashe, ba za su ce kuna hauka ba?
24
Amma in wani marar bi, ko jahili ya shigo sa’ad da kowa yana annabci, sai maganar kowa ta ratsa shi, za su shawo kansa yă gane cewa shi mai zunubi ne saboda abin da kowa yake faɗi,
25
asirin zuciyarsa kuma su bayyana a fili. Don haka, zai fāɗi a ƙasa yă yi wa Allah sujada yana cewa, “Lalle, Allah yana cikinku!”
Settings