Skip to content
1 Tarihi 19:6-15

1 Tarihi 19:6-15

6
Sa’ad da Ammonawa suka gane cewa sun zama abin wurin a kafan hancin Dawuda, Hanun da Ammonawa suka aika da talenti dubu na azurfa don su yi haya da kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi daga Aram-Naharayim, Aram Ma’aka da Zoba.
7
Suka yi hayar kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi dubu talatin da biyu, da kuma sarkin Ma’aka tare da mayaƙansa, waɗanda suka zo suka kafa sansani kusa da Medeba, yayinda Ammonawa suka tattaru daga garuruwansu suka fita yaƙi.
8
Da jin haka, Dawuda ya aiki Yowab tare da dukan mayaƙa masu yaƙi.
9
Ammonawa suka fito suka ja dāgā a ƙofar birninsu, yayinda sarakunan da suka zo, su kansu suka ware suna a fili.
10
Yowab ya ga cewa akwai dāgā a gabansa da bayansa; sai ya zaɓi waɗansu mayaƙa mafi kyau a Isra’ila ya sa su a kan Arameyawa.
11
Ya sa sauran mutanen a ƙarƙashin kulawar Abishai ɗan’uwansa, aka sa a kan Ammonawa.
12
Yowab ya ce, “In Arameyawa suka fi ni ƙarfi, sai ka kawo mini ɗauke da ni; amma in Ammonawa sun fi ka ƙarfi, sai in kawo maka ɗauke.
13
Ka yi ƙarfin hali bari mu yi yaƙi da jaruntaka saboda mutanenmu da biranen Allahnmu. Ubangiji zai yi abin da ya ga ya yi masa kyau.”
14
Sai Yowab da ƙungiyoyin mayaƙan da suke tare da shi suka matso don su yi yaƙi da Arameyawa, Arameyawan kuwa suka gudu a gabansa.
15
Sa’ad da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, sai su ma suka guda a gaban ɗan’uwansa Abishai suka shiga cikin birni. Sai Yowab ya koma Urushalima.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options