1 Tarihi 19:1-5
1
Ana nan, sai Nahash sarkin Ammonawa ya mutu, sai ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
2
Dawuda ya yi tunani, “Zan nuna jinƙai ga Hanun ɗan Nahash, domin mahaifinsa ya nuna alheri gare ni.” Saboda haka Dawuda ya aika da tawaga don yă yi wa Hanun ta’aziyya game da mahaifinsa. Sa’ad da mutanen Dawuda suka iso wurin Hanun a ƙasar Ammonawa don su ta’azantar da shi,
3
sai manyan Ammonawa suka ce wa Hanun, “Kana tsammani Dawuda yana girmama mahaifinka ne da ya aika mutanen nan wurinka su ta’azantar da kai? Ba mutanensa sun zo ne su bincika su kuma leƙi ƙasar su tumɓuke ta ba?”
4
Saboda haka Hanun ya kama mutanen Dawuda, ya yi musu aski, ya yayyanka rigunansu a daidai ɗuwawunsu, sa’an nan ya sallame su.
5
Da wani ya zo ya faɗa wa Dawuda game da mutanen, sai ya aiki ’yan aika su sadu da su, gama an ƙasƙantar da su ainun. Sarki ya ce, “Ku zauna a Yeriko har sai gemunku sun yi girma, sa’an nan ku dawo.”
Settings