Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wave Offering

30 ayoyi · 12 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Firist zai kaɗa ’yan raguna biyun a gaban Ubangiji, a matsayin hadaya ta kaɗawa, tare da burodin sababbin ’ya’yan fari na itatuwan. Tsarkaken hadaya ce ga Ubangiji ga firist.

  2. Firist zai karɓi hadaya ta gari don kishi daga hannuwanta, yă kaɗa shi a gaban Ubangiji sa’an nan yă kawo a bagade.

  3. Zai miƙa kwandon burodi marar yisti, yă kuma miƙa ɗan ragon hadaya ta salama tare da hadaya ta gari, da hadaya ta sha ga Ubangiji.

  4. “ ‘Bayan Banazaren ya aske gashinsa da ya alamta keɓewa, firist zai ɗauki dafaffiyar kafaɗar rago, da ƙosai da kuma waina daga cikin kwando waɗanda duka biyu marar yisti ne, yă sa su a tafin hannun keɓaɓɓen.

  5. “Har yanzu kuma duk abin da aka keɓe daga kyautai na dukan hadayun kaɗawa na Isra’ilawa naka ne. Na ba da wannan gare ka da ’ya’yanka maza da mata, a kowane lokaci. Kowa da yake da tsarki a gidanka zai iya ci.