Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Volcanoes: General references

15 ayoyi · 1 fanni

Ayoyi game da General references

  1. Sai kuka matso kusa, kuka tsaya a gindin dutse yayinda yana cin wuta har zuwa sararin sama, ga kuma baƙin gizagizai da kuma baƙin duhu.

  2. Sa’ad da kuka ji muryar daga duhu, yayinda dutsen yana cin wuta, dukan manyan kabilanku da dattawanku suka zo wurina.

  3. Duwatsu suka girgizu a gaban Ubangiji, Wannan na Sinai, a gaban Ubangiji, Allah na Isra’ila.

  4. Duwatsu sun narke kamar kakin zuma a gaban Ubangiji, a gaban Ubangijin dukan duniya.

  5. shi wanda ya dubi duniya, sai ta razana, wanda ya taɓa duwatsu, sai suka yi hayaƙi.

  6. Ka tsage sammanka, ya Ubangiji, ka sauko; ka taɓa duwatsu, domin su yi hayaƙi.

  7. Za a mai da rafuffukan Edom rami, ƙurarta za tă zama kibiritun farar wuta; ƙasarta za tă zama rami mai ƙuna!

  8. Ba za a kashe ta ba dare da rana; hayaƙinta za tă yi ta tashi har abada. Daga tsara zuwa tsara za tă zama kango; babu wani da zai ƙara wucewa ta wurin.

  9. Da ma za ka tsage sammai ka sauko, ai, da duwatsu za su yi rawar jiki a gabanka!

  10. Kamar sa’ad da wuta takan ci rassa ta sa ruwa ya tafasa, ka sauko ka sanar da sunanka ga abokan gābanka ka kuma sa al’ummai su yi rawan jiki a gabanka!

  11. Gama sa’ad da ka aikata abubuwan bantsoron da ba mu sa tsammani ba, ka sauko, duwatsu kuma suka yi rawar jiki a gabanka.

  12. “Ga shi, ina gāba da kai, ya ke dutse mai hallakarwa, wadda ta hallaka duniya duka,” in ji Ubangiji. “Zan miƙa hannuna gāba da ke, zan mirgina ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, zan maishe ki ƙonannen dutse.

  13. Duwatsu za su narke a ƙarƙashin ƙafafunsa, kamar kaki a gaban wuta, kwaruruka kuma za su ɓace, kamar ruwan da yake gangarowa daga tsauni.

  14. Duwatsu suna rawan jiki a gabansa tuddai kuma sun narke. Duniya da dukan abin da yake cikinta suna rawan jiki a gabansa.

  15. Wa zai iya tsaya wa fushinsa? Wa yake da ikon jimre wa zafin hasalarsa? Ana zuba fushinsa kamar wuta; aka kuma ragargaza duwatsu a gabansa.