Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Uzziel

8 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. ’Ya’yan Kohat maza, su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel. Kohat ya yi shekara 133.

  2. ’Ya’yan Uzziyel maza, su ne, Mishayel, Elzafan da Sitri.

  3. Sai Musa ya kira Mishayel da Elzafan, ’ya’yan Uzziyel kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan; ku ɗauki ’yan’uwanku waje da sansani, daga gaban wuri mai tsarki.”

  4. Mutum ɗari biyar na waɗannan mutane Simeyon, waɗanda Felatiya, Neyariya, Refahiya da Uzziyel, ’ya’yan Ishi maza suka jagorance, sun mamaye ƙasar tudu ta Seyir.

  5. ’Ya’yan Bela maza su ne, Ezbon, Uzzi, Uzziyel, Yerimot da Iri, su ne kawunan iyalai, kuma su biyar ne duka. Rubutaccen tarihin zuriyarsu ya nuna suna mazan da sun isa yaƙi 22,034.

  6. Game da Heman kuwa, daga ’ya’yansa maza. Bukkiya, Mattaniya, Uzziyel, Shebuwel, Yerimot; Hananiya, Hanani, Eliyata, Giddalti, Romamti-Ezer, Yoshbekasha, Malloti, Hotir da Mahaziyot.

  7. Daga iyalin Heman, Yehiyel da Shimeyi. Daga zuriyar Yedutun, Shemahiya da Uzziyel.

  8. Uzziyel ɗan Harhahiya, ɗaya daga cikin masu ƙeran zinariya ne ya yi gyare-gyaren sashe na biye; sai Hananiya, ɗaya daga cikin masu yin turare, ya yi gyare-gyaren biye da wannan. Suka gyara Urushalima har zuwa Katanga Mai Faɗi.