Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Tribe Of Dan: Plundered Michah of his idols and his ephod

5 ayoyi · 23 fannoni

Ayoyi game da Plundered Michah of his idols and his ephod

  1. Sai mutum biyar da suka leƙi asirin ƙasar suka shiga ciki suka ɗauke gunkin da aka sassaƙa, efod, sauran allolin gida da kuma gunki na zubi yayinda firist ɗin tare da mutane ɗari shida da suka yi ɗamarar yaƙi suna tsaye a bakin ƙofa.

  2. Sa’ad da waɗannan mutane suka shiga gidan Mika suka ɗauke gunkin da aka sassaƙa, efod, sauran allolin gida da kuma gunki na zubi, sai firist ya ce musu, “Me kuke yi?”

  3. Suka ce, “Ka yi shiru! Kada ka ce wani abu. Zo tare da mu, ka zama mahaifinmu da kuma firist. Bai fi maka ka yi wa kabila da kuma zuriya a Isra’ila aikin firist ba, da ka bauta wa iyali guda kawai?”

  4. Sai firist ya yi farin ciki. Ya ɗauki efod, sauran allolin gida da siffar da aka sassaƙa ya tafi tare da mutanen.

  5. Suka sa ’ya’yansu ƙanana a gaba, dabbobinsu da mallakansu a gabansu, suka juya suka tafi.