Skip to content

Laish

4 verses

33.2400, 35.6500 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Laish

  1. Saboda haka mutum biyar ɗin suka tashi suka iso Layish, inda suka ga mutane suna zamansu a huce, kamar Sidoniyawa, ba sa zato ga tsaro. Kuma da yake ƙasarsu ba ta bukata kome, suna da wadata. Suna kuma nesa da Sidoniyawa, ba sa kuma hulɗa da kowa.

  2. Sa’an nan mutum biyar ɗin nan da suka leƙi asirin ƙasar Layish suka ce wa ’yan’uwansu, “Kun san cewa ɗaya daga cikin gidajen nan yana da efod, waɗansu allolin iyali, siffar da aka sassaƙa da kuma gunki na zubi? To, kun san abin da za ku yi.”

  3. Sa’an nan suka ɗauko abin da Mika ya yi, da firist nasa, suka tafi Layish, suka fāɗa wa mutanen da suke zaman lafiya, ransu kuma a kwance. Suka fāɗa musu suka kuma ƙone birninsu.

  4. Suka sa wa birnin suna Dan, wato, sunan kakansu Dan, wanda aka haifa wa Isra’ila, ko da yake a dā ana kira birnin Layish.