Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Ishmaelites

32 ayoyi · 30 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. ku kawo ruwa don ƙishirwa; ku da kuke zama a Tema, ku kawo abinci don masu gudun hijira.

  2. Sun gudu daga takobi, daga takobin da aka janye, daga bakan da aka tanƙware da kuma daga zafin yaƙi.

  3. Ga abin da mai girma ya ce mini, “Cikin shekara ɗaya, kamar yadda bawan da aka bautar da shi bisa ga yarjejjeniya zai lissafta, dukan sojojin Kedar za su zo ga ƙarshe.

  4. Waɗanda suka yi rai na maharba, jarumawan Kedar, za su zama kaɗan.” Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa.

  5. Dedan, Tema, Buz da dukan waɗanda suke a manisantan wurare;

  6. dukan sarakunan Arabiya da dukan sarakunan baƙin da suke zama a hamada;

  7. dukan sarakunan Zimri, Elam da Mediya;