Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Feast of Sabbatical Year: Jews threatened for neglecting

6 ayoyi · 13 fannoni

Ayoyi game da Jews threatened for neglecting

  1. “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa na yi alkawari da kakanni-kakanninku sa’ad da na fitar da su daga Masar, daga ƙasar bauta. Na ce,

  2. ‘A kowace shekara ta bakwai dole kowannenku yă ’yantar da duk wani ɗan’uwa mutumin Ibraniyawa wanda aka sayar masa. Bayan ya yi muku hidima shekaru shida, dole ku bar shi yă tafi ’yantacce.’ Amma kakanninku ba su saurare ni ba, ba su ji ni ba.

  3. Bai daɗe ba da kuka tuba, kuka kuma yi abin da yake mai kyau a idona. Kowannenku ya yi shelar ’yanci ga ɗan’uwansa. Kun ma yi yarjejjeniya a gabana a gidan da ake kira da Sunana.

  4. Amma yanzu kun juya kun kuma ɓata sunana; kowannenku ya mayar da bayi maza da matan da kuka ’yantar su tafi inda suka ga dama. Kun sāke tilasta su su zama bayinku.

  5. “Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, kun yi mini rashin biyayya; ba ku yi shelar ’yanci don ’yan’uwanku ba. Saboda haka yanzu na yi muku shelar ’yanci in ji Ubangiji, ’yanci ga mutuwa ta takobi, annoba da kuma yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga sauran mulkokin duniya.

  6. Mutanen da suka keta alkawarina da ba su cika sharuɗan alkawarin da suka yi a gabana ba, zan yi da su kamar ɗan maraƙin da suka yanka biyu suka bi ta tsakiyarsa.