Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Call of God: Rejection by God

19 ayoyi · 33 fannoni

Ayoyi game da Rejection by God

  1. ka haɗa kai da mu, za mu kuwa raba abin da muka sato”

  2. ɗana, kada ka tafi tare da su, kada ka taka ƙafarka a hanyarsu;

  3. gama ƙafafunsu kan yi sauri ga yin zunubi, suna saurin yin kisankai.

  4. Ba shi da amfani a kafa tarko a idanun dukan tsuntsaye!

  5. Waɗannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko; ba sa kama kome, sai rayukansu!

  6. Dukan waɗanda suke neman ribar da ba a samu a hanya mai kyau; ƙarshen wannan yakan ɗauke rayukansu.

  7. Hikima tana kira da ƙarfi a kan titi, tana ɗaga muryarta a dandalin taron jama’a;

  8. tana kira da ƙarfi a kan tituna masu surutu, tana yin jawabinta a hanyoyin shiga gari.

  9. “Har yaushe ku da kuke marasa azanci za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci? Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku wawaye kuma ku ƙi ilimi?

  10. Da a ce kun saurari tsawatata, da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata in kuma sanar da ku tunanina.

  11. Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna,

  12. da yake kun ƙi dukan shawarata ba ku kuma yarda da tsawatata ba,

  13. Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku, zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku,

  14. sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri, sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa, sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku.

  15. “Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba; za su neme ni amma ba za su same ni ba.

  16. Da yake sun ƙi sani ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,

  17. da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,

  18. za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.

  19. Gama rashin hankalin marasa azanci zai kashe su, rashin kulawar wawaye kuma zai hallaka su;