Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Talebearer: General references

14 ayoyi · 1 fanni

Ayoyi game da General references

  1. “ ‘Kada ku yi ta yawo kuna yaɗa ƙarya a cikin mutanenku. “ ‘Kada ku yi wani abin da zai sa ran maƙwabcinku cikin hatsari. Ni ne Ubangiji.

  2. Zabura ta Dawuda. Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka? Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?

  3. Sai wanda ba shi da laifi kuma yana yin abin da yake daidai, wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa

  4. ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa, wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa mugunta ba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa,

  5. Gulma yakan lalace yarda, amma mutum mai aminci kan kiyaye asiri.

  6. Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali, mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa.

  7. Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne, amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa.

  8. Kalmomin mai gulma kamar abinci mai daɗi suke; sukan gangara zuwa can cikin gaɓoɓin mutum.

  9. Mai gulma yakan lalace yarda; saboda haka ka guji mutum mai yawan surutu.

  10. In ba itace wuta takan mutu; haka kuma in ba mai gulma ba za a yi faɗa ba.

  11. Kamar yadda gawayi yake ga murhu, itace kuma ga wuta, haka mutum mai neman faɗa yake ga faɗa.

  12. Kalmomin mai gulma suna kama da burodi mai daɗi; sukan gangara can cikin cikin mutum.

  13. Game da gwauraye masu ƙuruciya kuwa, kada ka sa su cikin wannan lissafi. Gama sa’ad da sha’awar jikinsu ta kāsa daurewa game da wa’adin da suka yi da Kiristi, sai su so yin aure.

  14. Ban da haka, sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida-gida. Ba kawai sun zama masu zaman banza ba, har ma sun zama masu gulma da masu shisshigi, suna faɗin abubuwan da bai kamata su faɗa ba.