Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Staves: Symbolic

8 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da Symbolic

  1. Saboda haka na yi kiwon garken da za a yanka, musamman garken da ake zalunta. Sai na ɗauki sanduna biyu na kira ɗaya Tagomashi, ɗaya kuma Haɗinkai, sai na yi kiwon garken.

  2. Cikin wata guda na kawar da makiyayan nan uku. Garken suka ƙi ni, na kuwa gaji da su

  3. na ce, “Ba zan zama makiyayinku ba. Bari masu mutuwa su mutu, masu hallaka kuma su hallaka. Bari waɗanda suka ragu su ci naman juna.”

  4. Sai na ɗauki sandana mai suna Tagomashi na karya shi, na janye alkawarin da na yi da dukan al’ummai.

  5. An janye shi a ranan nan, saboda haka garken da yake cikin wahala masu kallona sun san cewa maganar Ubangiji ce.

  6. Na faɗa musu cewa, “In kun ga ya fi kyau, ku biya ni; in kuwa ba haka ba, ku riƙe.” Saboda haka suka biya ni azurfa talatin.

  7. Sai Ubangiji ya ce mini, “Jefar da shi cikin ma’aji,” Lada mai kyau da aka yi cinikina ne! Saboda haka sai na ɗauki azurfa talatin ɗin na jefa su cikin gidan Ubangiji don a sa cikin ma’aji.

  8. Sai na karya sandana na biyu mai suna Haɗinkai, ta haka na karya ’yan’uwantakar da take tsakanin Yahuda da Isra’ila.