Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sihor

4 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Daga Kogin Shihor a gabashin Masar zuwa sashen Ekron a arewa, dukan wannan ƙasa ana lissafta ta a cikin ƙasar Kan’aniyawa, ko da yake tana a sashen da sarakuna biyar na Filistiyawa na Gaza, Ashdod, Ashkeloniyawa, Gat da Ekron; na Awwiyawa.

  2. Saboda haka Dawuda ya tattara dukan Isra’ilawa, daga Kogin Shihor a Masar zuwa Lebo Hamat, don su kawo akwatin alkawarin Allah daga Kiriyat Yeyarim.

  3. A manyan ruwaye hatsin Shihor suka iso; girbin Nilu ne kuɗin shiga na Taya ta kuma zama kasuwar al’ummai.

  4. To, me ya sa za ka Masar don shan ruwa daga Shihor? Kuma me ya sa za ka Assuriya don shan ruwa daga Kogi?