Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Shebna: 1. A scribe of Hezekiah

8 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da 1. A scribe of Hezekiah

  1. Suka kira sarki, sai Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci suka je wurinsu.

  2. Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, da Shebna, da Yowa suka ce wa jagoran dakarun, “Muna roƙonka ka yi wa bayinka magana da harshen Arameyik da yake muna ji. Kada ka yi mana magana da Yahudanci domin kada mutanen da suke bisa katanga su ji!”

  3. Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf, marubuci, suka je wurin Hezekiya da tufafinsu a kece, suka faɗa masa abin da shugaban sojojin ya faɗa.

  4. Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna marubuci da shugabannin firistoci, dukansu sanye da tufafin makoki, zuwa wurin annabi Ishaya ɗan Amoz.

  5. Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci suka fita zuwa wurinsa.

  6. Sai Eliyakim, Shebna da Yowa suka ce wa sarkin yaƙin, “Ka yi haƙuri ka yi wa bayinka magana da Arameyanci, da yake muna jinsa. Kada ka yi mana magana da Yahudanci a kunnen mutanen da suke kan katanga.”

  7. Sai Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, Shebna magatakarda, da kuma Yowa ɗan Asaf marubuci suka tafi wurin Hezekiya, da rigunansu a kyakkece, suka kuwa faɗa masa abin da sarkin yaƙin ya yi ta farfaɗa.

  8. Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna magatakarda da kuma manyan firistoci, duka sanye da tsummoki, wurin Ishaya ɗan Amoz.