Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Shalmaneser

7 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Shalmaneser sarkin Assuriya ya kawo wa Hosheya wanda dā abokin tarayyarsa ne, hari har Hosheya ya biya shi haraji.

  2. Amma sarkin Assuriya ya gane cewa Hosheya mai cin amana ne, gama ya aika da wakilai wurin So sarkin Masar, ya kuma daina aika wa sarkin Assuriya haraji yadda ya saba yi kowace shekara. Saboda haka Shalmaneser ya kama shi ya sa a kurkuku.

  3. Sarkin Assuriya ya kai wa ƙasar Hosheya gaba ɗaya farmaki, ya kewaye Samariya na tsawon shekara uku.

  4. A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, sarkin Assuriya ya ci Samariya da yaƙi ya kuma kwashe Isra’ilawa zuwa Assuriya. Ya tsugunar da su a Hala, da a Gozan a bakin Kogin Habor da kuma a garuruwan Medes.

  5. A shekara ta huɗu ta Hezekiya, wato, shekara ta bakwai ke nan ta mulkin Hosheya ɗan Ela sarkin Isra’ila; Shalmaneser Sarkin Assuriya ya tasam ma Samariya da yaƙi; ya kewaye ta.

  6. A ƙarshen shekara ta uku, Assuriyawa suka ci Samariya da yaƙi. An ci Samariya da yaƙi a shekara ta shida ta mulki Hezekiya, wanda ya zo daidai da shekara ta tara ta mulkin Hosheya sarkin Isra’ila.

  7. Sarkin Assuriya ya kwashe Isra’ila zuwa Assuriya ya zaunar da su a Hala, da Gozan a kogin Habor da kuma garuruwan Medes.