Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ostriches

15 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. mujiya mai ƙaho, jimina, shaho, da kowane irin shaho,

  2. jimina, ƙururu, bubuƙuwa, kowane irin shaho,

  3. Na zama ɗan’uwan diloli, na zama abokan mujiyoyi.

  4. “Fikafikan jimina suna bugawa cike da farin ciki amma ba za su gwada kansu da fikafikan da na shamuwa ba.

  5. Tana sa ƙwai nata a ƙasa kuma ta bar su su yi ɗumi a cikin ƙasa,

  6. ba tă damu ko za a taka su a fasa su, ko waɗansu manyan dabbobi za su tattake su.

  7. Tana tsananta wa ’ya’yanta kamar ba nata ba ba tă damu da wahalar da ta sha ba.

  8. Gama Allah bai ba ta hikima ba ko kuma iya fahimta.

  9. Duk da haka sa’ad da ta buɗe fikafikanta ta shara da gudu tana yi wa doki da mai hawansa dariya.

  10. Amma halittun hamada za su kwanta a can, diloli za su cika gidajenta; a can mujiyoyi za su zauna, a can kuma awakin jeji za su yi ta tsalle.

  11. Ƙayayuwa za su mamaye fadodinta ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za su cika kagaranta. Za tă zama mazaunin diloli da gida don mujiyoyi.

  12. Namun jeji suna girmama ni, diloli da mujiyoyi ma haka, domin na tanada musu ruwa a hamada da rafuffuka a ƙeƙasasshiyar ƙasa, don a ba da abin sha ga mutanena, zaɓaɓɓuna,

  13. “Saboda haka halittun hamada da kuraye za su zauna a can, a can kuma mujiya za tă zauna. Ba za a ƙara zauna ko a yi zama a cikinta ba daga tsara zuwa tsara.

  14. Ko diloli suna ba ’ya’yansu nono su sha, amma mutanena sun zama marasa zuciya kamar jiminai a cikin jeji.

  15. Saboda wannan zan yi baƙin ciki, in yi kuka; zan yi tafiya ba takalmi, zan tuɓe, in kuma yi tafiya tsirara. Zan yi kuka kamar dila, in yi baƙin ciki kamar mujiya.