Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Orphan

49 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Kada ku ci zalin gwauruwa, ko maraya.

  2. In kuka yi haka, idan kuma suka yi kuka gare ni, zan ji kukansu.

  3. Zan husata, in kuma kashe ku da takobi; matanku kuma, su ma su zama gwauraye, ’ya’yanku kuwa su zama marayu.

  4. Yakan tsare marayu da gwauraye, yana ƙaunar baƙon da yake zama a cikinku, yana ba su abinci da tufafi.

  5. A ƙarshen kowace shekara uku, ku kawo dukan zakkarku na amfanin gona na wannan shekara, ku ajiye su a cikin birane,

  6. saboda Lawiyawa (waɗanda ba su da rabo ko gādo na kansu) da baƙo, da marayu, da kuma gwauraye, waɗanda suke zama a biranenku, su zo su ci su ƙoshi, ta haka Ubangiji Allahnku zai albarkace ku cikin dukan ayyukan hannuwanku.

  7. Ku kuma yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da ya zaɓa a matsayin mazauni don Sunansa, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da Lawiyawan cikin biranenku, har ma da baƙi, da marayu, da kuma gwaurayen da suke zama a cikinku.

  8. Ku yi farin ciki a Bikinku, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da Lawiyawa, da baƙi, da marayu, da kuma gwaurayen da suke zama a cikin biranenku.

  9. Ba za ku danne hakkin baƙon da yake zama a cikinku ko na marayu ba, ba za ku ɗauki rigar matar da mijinta ya mutu a matsayin jingina ba.

  10. Ku tuna dā ku bayi ne a Masar, Ubangiji Allahnku kuwa ya fisshe daga can. Shi ya sa na umarce ku ku yi wannan.

  11. Sa’ad da kuke girbi a gonarku, sai kuka manta da dami, kada ku koma don ku ɗauka. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa, saboda Ubangiji Allahnku yă albarkace ku a cikin dukan aikin hannuwanku.

  12. Sa’ad da kuka kakkaɓe ’ya’yan zaitun daga itatuwanku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa.

  13. Sa’ad da kuka yi girbin inabi a gonar inabinku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa.

  14. Ku tuna dā ku bayi ne Masar. Shi ya sa na umarce ku ku yi wannan.

  15. Sa’ad da kuka gama fitar da kashi ɗaya bisa goma na dukan amfanin gona a shekara ta uku, shekarar zakka, za ku ba da su ga Balawe, baƙo, maraya da kuma gwauruwa, don su ci a cikin garuruwanku su ƙoshi.

  16. Sa’an nan ku faɗa wa Ubangiji Allahnku, “Na cire tsattsarkan rabo daga gidana na kuma ba wa Balawe, baƙo, maraya da gwauruwa, bisa ga dukan abin da ka umarta. Ban ja gefe daga umarnanka ko in manta da wani a cikinsu ba.

  17. “La’ananne ne mutumin da ya yi rashin adalci ga baƙo, maraya ko gwauruwa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  18. Kukan yi ƙuri’a a kan marayu ku kuma sayar da abokinku.

  19. Ka kori gwauraye hannu wofi, ka kuma karya ƙarfin marayu.

  20. Suna ƙwace wa marayu jakunansu suna kuma ƙwace wa gwauruwa sa don suna binta bashi.

  21. Ana ƙwace jinjiri mai shan mama; ana ƙwace ɗan yaron matalauci don biyan bashi.

  22. domin na ceci matalauta waɗanda suka nemi taimako, da marasa mahaifi waɗanda ba su da wanda zai taimake su.

  23. Mutumin da yake bakin mutuwa ya sa mini albarka. Na faranta wa gwauruwa zuciya.

  24. “In na hana wa matalauta abin da suke so, ko kuma in sa idanun gwauruwa su yi nauyi don kuka,

  25. in na ajiye burodina don kaina kaɗai, ban kuwa ba wa marayu abinci sa’ad da suke jin yunwa,