Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Neighbor

70 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba.

  2. “In ka ga saniyar abokin gābanka, ko jakinsa ya ɓace, ka yi ƙoƙari ka mai da shi wurinsa.

  3. In ka ga jakin wani maƙiyinka ya fāɗi a ƙarƙashin kayan da ya ɗauka, kada ka bar shi can, ka yi ƙoƙari ka taimake shi.

  4. “In wani ya yi zunubi bai kuma yi aminci ga Ubangiji ba, wato, ta wurin yin wa abokin zamansa karya game da ajiyar da abokin ya ba shi amana, ko a kan wani alkawarin da suka yi wa juna, ko kuwa a kan yă cuci abokin,

  5. ko kuma idan ya sami abin da ya ɓace amma ya yi ƙarya cewa bai samu ba. Ko ya yi rantsuwar ƙarya a kan duk irin abubuwan da akan aikata na laifi,

  6. sa’ad da mutum ya yi irin laifin nan, ya kuwa tabbata mai laifi ne, to, sai yă komar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta.

  7. Zai mai da abin da ya yi rantsuwar ƙarya a kai. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har yă ƙara kashi ashirin bisa ɗari na abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa.

  8. “ ‘Kada ku zalunci maƙwabcinku, ko ku yi masa ƙwace. “ ‘Kada ku riƙe albashin ma’aikaci yă kwana.

  9. “ ‘Kada ku yi ta yawo kuna yaɗa ƙarya a cikin mutanenku. “ ‘Kada ku yi wani abin da zai sa ran maƙwabcinku cikin hatsari. Ni ne Ubangiji.

  10. “ ‘Kada ka yi ƙiyayyar ɗan’uwanka a zuciya. Ka tsawata wa maƙwabcinka da gaske don kada ka sami rabo cikin laifinsa.

  11. “ ‘Kada ka nemi yin ramuwa, ko ka riƙe wani cikin mutanenka a zuciya, amma ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ni ne Ubangiji.

  12. In kun ga saniya ko tunkiyar ɗan’uwanku wadda ta ɓace, kada ku ƙyale ta, amma ku tabbata kun komar da ita gare shi.

  13. In ɗan’uwan ba ya zama kusa da ku, ko kuwa ba ku san shi ba, sai ku kai ta gida ku ajiye ta sai ya zo nemanta. Sa’an nan ku ba shi ita.

  14. Ku yi haka in kun sami jakin ɗan’uwanku, ko rigarsa, ko kowane abin da ya ɓace. Kada ku ƙyale shi.

  15. In kuka ga jakin ɗan’uwanku, ko saniyarsa ya fāɗi a kan hanya, kada ku ƙyale shi. Ku taimaka, ku tā da shi.

  16. Zabura ta Dawuda. Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka? Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?

  17. Sai wanda ba shi da laifi kuma yana yin abin da yake daidai, wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa

  18. ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa, wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa mugunta ba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa,

  19. Kada ka ce wa maƙwabcinka “Ka yă dakata sai gobe,” idan kana iya taimakonsa yanzu.

  20. Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka, wanda yake zama da aminci kusa da kai.

  21. “Irin azumin da na zaɓa shi ne, a kunce sarƙoƙin rashin adalci a kuma kunce igiyoyin karkiya, a ’yantar da waɗanda ake zalunta a kuma kakkarye kowace karkiya?

  22. Ba shi ne ku rarraba abincinku da mayunwata ku kuma tanada wa matalauta masu yawo mahalli, sa’ad da kuka ga wanda yake tsirara, ku yi masa sutura, kada kuma ku ba wa namanku da jininku baya?

  23. Sa’an nan haskenku zai keto kamar ketowar alfijir, warkarwarku kuma zai bayyana nan da nan; sa’an nan adalcinku zai tafi a gabanku, ɗaukakar Ubangiji kuma zai tsare ku daga baya.

  24. Sa’an nan za ku yi kira, Ubangiji kuma zai amsa; za ku yi kuka don neman taimako, zai kuwa ce ga ni nan. “In kuka kawar da karkiyar zalunci, kuka daina nuna wa juna yatsa da kuma faɗar mugayen maganganu,

  25. in kuma kuka ɗauki lokaci kuka ƙosar da mayunwata kuka kuma biya bukatun waɗanda suke shan tsanani, sa’an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu darenku kuma zai zama kamar tsakar rana.