Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Nazarites

32 ayoyi · 20 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Amma kuka sa keɓaɓɓun suka sha ruwan inabi kuka kuma umarci annabawa kada su yi annabci.

  2. gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa.

  3. Bulus kuwa ya ci gaba da zama a Korint na ’yan kwanaki. Sa’an nan ya bar ’yan’uwa ya shiga jirgin ruwa zuwa Suriya tare da Firiskila da Akwila. Kafin ya tashi, ya aske kansa a Kenkireya saboda alkawarin da ya yi.

  4. Ka ɗauki waɗannan mutane, ka tafi da su ku tsarkaka gaba ɗaya, ka kuma biya musu kome don su samu su yi aski. Ta haka kowa zai sani babu gaskiya a waɗannan rahotanni game da kai, za a kuma ga cewa kai kanka kana kiyaye dokar.

  5. Saboda haka, “Sai ku fito daga cikinsu, ku keɓe kanku, in ji Ubangiji. Kada ku taɓa wani abu marar tsabta, zan kuma karɓe ku.”

  6. Irin wannan babban firist ne muke bukata, shi mai tsarki ne, marar aibi, mai tsabta, ba kamar mu masu zunubi ba sam. An ɗaukaka shi fiye da kome a sama.

  7. Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.