Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Nail

5 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Amma Yayel, matar Heber, ta ɗauki turken tenti da guduma ta tafi wurinsa da sauri sa’ad da yake barci saboda gajiya. Ta kafa masa turken a gindin kunnensa ta haɗa shi da ƙasa, har ya mutu.

  2. Ya tanada ƙarfe mai yawa don ƙusoshi saboda ƙyamaren hanyoyin shiga da kuma saboda mahaɗai, da ƙarin tagulla fiye da ƙirge.

  3. Nauyin ƙusoshin ya kai shekel hamsin na zinariya. Ya kuma shafe benaye da zinariya zalla.

  4. Masassaƙi yakan ƙarfafa maƙerin zinariya, kuma shi mai gyara da guduma ya yi sumul yakan ƙarfafa mai harhaɗawa. Ya ce game da haɗin, “Ya yi kyau.” Yakan buga ƙusoshi su riƙe gunkin don kada yă fāɗi.

  5. Sukan yi masa ado da azurfa da kuma zinariya; sukan ɗauki guduma su kafa shi da ƙusoshi, don kada yă fāɗi.