Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Minister (2): Joseph

5 ayoyi · 9 fannoni

Ayoyi game da Joseph

  1. Za ka shugabanci fadata, kuma dukan mutanena za su zama a ƙarƙashinka. Da sarauta kaɗai zan fi ka girma.”

  2. Saboda haka Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Ga shi na sa ka zama shugaban dukan ƙasar Masar.”

  3. Sa’an nan Fir’auna ya zare zoben sarauta daga yatsarsa, ya sa shi a yatsan Yusuf. Ya sanya masa rigar lallausan lilin, ya kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa.

  4. Ya sa shi ya hau keken yaƙi a matsayi mai binsa na biyu, mutane kuwa suka yi shela a gabansa suna cewa, “A ba da hanya!” Ta haka ya sa shi shugaba a kan dukan ƙasar Masar.

  5. Sa’an nan Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Ni ne Fir’auna, amma in ba tare da umarninka ba, ba wanda zai ɗaga hannu ko ƙafa a cikin dukan Masar.”