Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Leprosy

61 ayoyi · 50 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “ ‘In zuriyar Haruna yana da kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga,

  2. Ubangiji ya ce wa Musa,

  3. “Ka umarci Isra’ilawa su kori duk wanda yake da ciwon fatan jiki, ko mai ɗiga na kowane iri, ko wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, daga cikin sansani.

  4. Ka kori maza da mata ma; ka kai su bayan sansani domin kada su ƙazantar da sansani inda nake zama a cikinsu.”

  5. Da Elisha mutumin Allah ya ji cewa sarkin Isra’ila ya yayyage tufafinsa, sai ya aika masa da wannan saƙo, “Don me za ka yayyage tufafinka? Ka sa mutumin yă zo wurina, zai kuwa san cewa akwai annabi a Isra’ila.”

  6. Saboda haka Na’aman ya tafi da dawakansa da keken yaƙinsa, ya tsaya a ƙofar gidan Elisha.

  7. Sai Elisha ya aika ’yan saƙo su ce masa, “Je, ka nutse sau bakwai a Urdun, fatar jikinka za tă koma daidai, ka kuma tsarkaka.”

  8. Amma Na’aman ya tashi daga can da fushi yana cewa, “Na yi tsammani zai fito ne wurina yă tsaya, yă yi kira bisa ga sunan Ubangiji Allahnsa, yă kaɗa hannunsa inda kuturtar take, yă warkar da ni.

  9. Ashe, Amana da Farfa, kogunan da suke Damaskus, ba su fi dukan ruwan da suke Isra’ila ba? Me zai sa ba zan nutse cikinsu in tsarkaka ba?” Sai ya juya ya yi tafiyarsa da fushi.

  10. Sai bayin Na’aman suka je kusa da shi suka ce, “Baba, da a ce annabin ya ce ka yi wani abu mai wuya, da ba za ka yi ba? Balle fa cewa kawai ya yi, ‘Ka yi wanka ka kuma tsarkaka’!”

  11. Saboda haka Na’aman ya je ya nutse sau bakwai a Urdun, yadda mutumin Allah ya ce masa, sai fatarsa ta koma kamar ta ɗan yaro.