Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Labor

29 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kwana shida za ka yi dukan aikinka,

  2. amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai.

  3. Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.

  4. Kada ku zalunci ɗan ƙodago matalauci da mabukaci, ko da shi ɗan’uwanku ne mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a cikin garuruwanku.

  5. Ku biya kuɗin aikinsa kowace rana kafin fāɗuwar rana, domin shi matalauci ne, yana kuma sa rai a kan wannan hakkin ne, don kada ya yi wa Ubangiji kuka a kanku, har yă zama laifi a gare ku.

  6. “Mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da sassafe don yă yi hayar mutane su yi aiki a gonar inabinsa.

  7. Ya yarda yă biya su dinari guda a yini, sai ya tura su gonar inabinsa.

  8. “Wajen sa’a ta uku, ya fita sai ya ga waɗansu suna tsattsaye a bakin kasuwa ba sa kome.

  9. Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi gonar inabina ku yi aiki, zan kuwa biya ku abin da ya dace.’

  10. Saboda haka suka tafi. “Ya sāke fita a sa’a ta shida da kuma sa’a ta tara, ya sāke yin haka.

  11. Wajen sa’a ta goma sha ɗaya, ya sāke fita, ya tarar da waɗansu har yanzu suna tsattsaye. Ya tambaye su, ‘Don me kuke yini tsattsaye a nan ba kwa kome?’

  12. “Suka amsa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’ “Ya ce musu, ‘Ku ma ku je ku yi aiki a gonar inabina.’

  13. “Sa’ad da yamma ta yi, sai mai gonar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kira ma’aikatan, ka biya su hakkin aikinsu, fara daga waɗanda aka ɗauke su a ƙarshe har zuwa na farko.’

  14. “Ma’aikatan da ka ɗauka wajen sa’a ta goma sha ɗaya suka zo, kowannensu kuwa ya karɓi dinari guda.

  15. Saboda haka da waɗanda aka ɗauka da fari suka zo, sun zaci za su sami fiye da haka. Amma kowannensu ma ya karɓi dinari guda.

  16. Sa’ad da suka karɓa, sai suka fara yin gunaguni a kan mai gonar.

  17. Suna cewa, ‘Waɗannan mutanen da aka ɗauka a ƙarshe sun yi aikin sa’a ɗaya ne kawai, ka kuma mai da su daidai da mu da muka yini muna faman aiki, muka kuma sha zafin rana.’

  18. “Amma ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Aboki, ban cuce ka ba. Ba ka yarda ka yi aiki a kan dinari guda ba?

  19. Ka karɓi hakkinka ka tafi. Ni na ga damar ba waɗannan na ƙarshe daidai da yadda na ba ka.

  20. Ba ni da ikon yin abin da na ga dama da kuɗina ne? Ko kana kishi saboda ni mai kyauta ne?’

  21. Ku mai da wannan burinku na yi natsattsiyar rayuwa, kuna mai da hankali ga sha’anin da yake gabanku, kuna kuma yin aiki da hannuwanku, kamar dai yadda muka gaya muku,

  22. don rayuwanku ta kullum ta zama da mutunci ga waɗanda suke na waje don kuma kada ku dogara a kan kowa.

  23. Gama ku kanku kun san yadda ya kamata ku bi gurbinmu. Ba mu yi zaman banza sa’ad da muke tare da ku ba,

  24. ba mu kuwa ci abincin kowa ba tare da ba mu biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki dare da rana, muna fama muna wahala kuma don kada mu nawaita wa waninku.

  25. Mun yi wannan, ba don ba mu da ’yancin karɓar irin taimakon nan ba ne, sai dai domin mu zama gurbin da za ku bi.