Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Judgment: The general judgment

146 ayoyi · 1 fanni

Ayoyi game da The general judgment

Tace bisa littafi
  1. “In da na danne wa bayina maza da mata hakkinsu, sa’ad da suke da damuwa da ni,

  2. me zan yi lokacin da Allah ya tuhume ni? Me zan ce lokacin da ya tambaye ni?

  3. Shi wanda ya yi ni a cikin uwata ba shi ne ya yi su ba? Ba shi ne ya yi mu a cikin uwayenmu ba?

  4. Allahnmu yana zuwa ba kuwa zai yi shiru ba; wuta mai cinyewa a gabansa, babban hadari kuma ya kewaye shi.

  5. Ya kira sammai da suke bisa, da duniya, don yă shari’anta mutanensa.

  6. “Ku tattara mini shafaffuna, waɗanda suka yi alkawari da ni ta wurin hadaya.”

  7. Sammai kuwa sun yi shelar adalcinsa gama Allah kansa alƙali ne. Sela

  8. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai sami rabo a laifin mahaifi ba, mahaifi ba zai sami rabo a laifi ɗa ba. Adalcin adali zai zama nasa, muguntar mugu za tă koma kansa.

  9. “Amma in mugun mutum ya juya daga dukan zunubin da ya aikata ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina ya kuwa yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba.

  10. Babu laifin da ya yi da za a tuna da su. Saboda abubuwan adalcin da ya aikata, zai rayu.

  11. Ina jin daɗin mutuwar mugu ne? In ji Ubangiji Mai Iko Duka. A maimako, ban fi jin daɗi sa’ad da suka juyo daga hanyoyinsu suka rayu ba?

  12. “Amma in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya yi zunubi ya kuma aikata abubuwa masu banƙyamar da mugun mutum ke aikatawa, zai rayu? Babu abubuwan adalcin da ya aikata da za a tuna da su. Saboda rashin amincinsa da kuma saboda zunubai da ya yi, zai mutu.

  13. “Duk da haka kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Ka ji, ya gidan Isra’ila. Hanyata ba daidai ba ce?

  14. In mai adalci ya juye daga adalcinsa ya yi zunubi, zai mutu saboda wannan; saboda zunubin da ya yi, zai mutu.

  15. Amma in mugun mutum ya juye daga muguntarsa ya kuma yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, zai ceci ransa.

  16. Domin ya lura da dukan laifofin da ya yi ya kuma juye daga gare su, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba.

  17. “Ina cikin dubawa, “sai aka ajiye kursiyoyi, sai ga wani wanda yake tun fil azal ya zauna a mazauninsa. Rigarsa ta yi fari fat kamar ƙanƙara; gashin kansa sun yi fari kamar ulu. Kursiyinsa kuma harshen wuta, dukan ƙafafun kursiyin masu kama da keken yaƙin, wuta ne.

  18. Kogin wuta yana gudu, yana fitowa daga gabansa. Dubun dubbai sun yi masa hidima; dubu goma sau dubu goma sun tsaya a gabansa. Aka zauna don shari’a, aka kuma buɗe littattafai.

  19. Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’

  20. Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’

  21. Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa.

  22. Gama ta wurin kalmominka za a kuɓutar da kai, kuma ta wurin kalmominka za a hukunta ka.”

  23. Mutanen Ninebe za su tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, su kuwa hukunta shi; don sun tuba saboda wa’azin Yunana, yanzu kuwa ga wanda ya fi Yunana girma a nan.

  24. Sarauniyar Sheba za tă tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, tă kuwa hukunta shi; don ta zo daga ƙarshen duniya, ta saurari hikimar Solomon, yanzu kuwa ga wanda ya fi Solomon girma a nan.

  25. “Kamar yadda aka tattara ciyayin aka kuma ƙone a wuta, haka zai zama a ƙarshen zamani.