Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Husbands: To dwell with them for life

7 ayoyi · 15 fannoni

Ayoyi game da To dwell with them for life

  1. Waɗansu Farisiyawa suka zo wurinsa don su gwada shi. Suka yi tambaya suka ce, “Daidai ne mutum yă saki matarsa saboda wani dalili da kuma a kan kowane dalili?”

  2. Ya amsa ya ce, “Ba ku taɓa karantawa ba ne cewa, a farkon halitta, Mahalicci ‘ya yi su namiji da ta mace,’

  3. ya kuma ce, ‘Saboda wannan dalili, namiji zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa yă manne wa matarsa, biyun kuwa su zama jiki guda’?

  4. Ta haka, ba sa ƙara zama biyu, sai dai ɗaya. Saboda haka abin da Allah ya haɗa fa, kada mutum yă raba.”

  5. Suka yi tambaya, suka ce, “To, me ya sa Musa ya umarta cewa mutum yă ba wa matarsa takardar saki, yă kuma kore ta?”

  6. Yesu ya amsa ya ce, “Musa ya ba ku izini ku saki matanku saboda taurin zuciyarku ne. Amma ba haka yake ba daga farko.

  7. Ina faɗa muku cewa duk wanda ya saki matarsa, sai dai a kan rashin aminci a cikin aure, ya kuwa auri wata, ya yi zina ke nan.”