Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Hospitality: General references

52 ayoyi · 28 fannoni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. “ ‘Sa’ad da baƙo yana zama tare da ku a ƙasarku, kada ku wulaƙanta shi.

  2. Dole ku ɗauki baƙon da yake zama tare da ku kamar haifaffe ɗan ƙasa. Ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  3. Yakan tsare marayu da gwauraye, yana ƙaunar baƙon da yake zama a cikinku, yana ba su abinci da tufafi.

  4. Sai ku ƙaunaci baƙi, gama dā ku ma baƙi ne a ƙasar Masar.

  5. Sa’ad da kuka gama fitar da kashi ɗaya bisa goma na dukan amfanin gona a shekara ta uku, shekarar zakka, za ku ba da su ga Balawe, baƙo, maraya da kuma gwauruwa, don su ci a cikin garuruwanku su ƙoshi.

  6. Sa’an nan ku faɗa wa Ubangiji Allahnku, “Na cire tsattsarkan rabo daga gidana na kuma ba wa Balawe, baƙo, maraya da gwauruwa, bisa ga dukan abin da ka umarta. Ban ja gefe daga umarnanka ko in manta da wani a cikinsu ba.

  7. Hikima ta gina gidanta; ta yi ginshiƙansa bakwai.

  8. Ta shirya abincinta gauraye da ruwan inabinta; ta kuma shirya teburinta.

  9. Ta aiki bayinta mata, tana kuma kira daga wurare masu tsayi na birnin.

  10. “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo nan ciki!” Tana faɗa wa marasa hankali.

  11. “Ku zo, ku ci abincina da ruwan inabin da na gauraye.

  12. Kada ka ci abincin mai rowa, kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi;

  13. gama shi wani irin mutum ne wanda kullum yana tunani game da tsadar abincin. Zai ce maka, “Ci ka sha,” amma zuciyarsa ba ta tare da kai.

  14. Za ka yi amai ɗan abin da ka ci dukan daɗin bakinka kuwa zai tafi a banza.

  15. “Irin azumin da na zaɓa shi ne, a kunce sarƙoƙin rashin adalci a kuma kunce igiyoyin karkiya, a ’yantar da waɗanda ake zalunta a kuma kakkarye kowace karkiya?

  16. Ba shi ne ku rarraba abincinku da mayunwata ku kuma tanada wa matalauta masu yawo mahalli, sa’ad da kuka ga wanda yake tsirara, ku yi masa sutura, kada kuma ku ba wa namanku da jininku baya?

  17. “Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya bikin auren ɗansa.

  18. Sai ya aiki bayinsa su kira waɗanda aka gayyata zuwa bikin, amma waɗanda aka ce su zo bikin, suka ƙi zuwa.

  19. “Sai ya sāke aiken waɗansu bayi ya ce, ‘Ku ce wa waɗanda aka gayyata cewa na shirya abinci. An yanka bijimai da shanun da aka yi kiwo, kome a shirye yake. Ku zo bikin auren mana.’

  20. “Amma ba su kula ba, suka kama gabansu, ɗaya ya tafi gonarsa, ɗaya kuma ya tafi kasuwancinsa.

  21. Sauran suka kama bayinsa suka wulaƙanta su, suka kuma kashe su.

  22. Sai sarkin ya yi fushi. Ya aiki mayaƙansa suka karkashe masu kisankan nan, aka kuma ƙone birninsu.

  23. “Sa’an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin aure fa ya shiryu, sai dai mutanen da na gayyata ba su dace ba.

  24. Ku bi titi-titi ku gayyato duk waɗanda kuka gani, su zo bikin.’

  25. Saboda haka bayin suka bi titi-titi, suka tattaro duk mutanen da suka samu, masu kirki da marasa kirki, zauren bikin ya cika makil da baƙi.