Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Holiness: General references

147 ayoyi · 51 fannoni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan Ubangiji ya yi magana da Haruna ya ce,

  2. “Kai da ’ya’yanka maza, ba za ku sha ruwan inabi ko wani abu mai sa jiri ba a duk sa’ad da za ku shiga cikin Tentin Sujada, in ba haka ba za ku mutu. Wannan dawwammamiyar farilla ce wa tsararraki masu zuwa.

  3. Dole ku bambanta tsakanin mai tsarki da marar tsarki, tsakanin marar tsabta da mai tsabta,

  4. Ni ne Ubangiji Allahnku; ku tsarkake kanku ku kuma zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani halittar da take rarrafe a ƙasa.

  5. Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da ku daga Masar don in zama Allahnku; saboda haka ku zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne.

  6. Shi ne ya sa Isra’ilawa suka kāsa yin tsayayya da abokan gābansu; suka juya suka gudu domin za a hallaka su. Ba zan sāke kasancewa tare da ku ba sai in kun hallaka duk abin da aka keɓe don hallaka.

  7. “Tashi, ka je ka tsarkake mutane. Ka ce musu su tsarkake kansu, su yi shiri domin gobe; gama ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, a cikinku akwai abubuwan da aka keɓe, ya Isra’ilawa. Ba za ku iya yin tsayayya da abokan gābanku ba sai in kun rabu da abubuwan nan da aka haramta.

  8. Zabura ta Dawuda. Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka? Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?

  9. Sai wanda ba shi da laifi kuma yana yin abin da yake daidai, wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa

  10. ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa, wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa mugunta ba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa,

  11. wanda yake ƙin mugun mutum amma yakan girmama masu tsoron Ubangiji, yakan cika alkawarinsa ko da ma ya zafe shi,

  12. wanda yake ba da rance ba tare da ruwa ba kuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi. Shi wanda yake yin waɗannan abubuwa ba zai taɓa jijjiguwa ba.

  13. Wa zai iya hawan tudun Ubangiji? Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?

  14. Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya, wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.

  15. Zai sami albarka daga Ubangiji da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.

  16. Albarka ta tabbata ga waɗanda rayuwarsu ba ta da abin zargi, waɗanda suke tafiya bisa ga dokar Ubangiji.

  17. Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu.

  18. Ba sa yin wani abin da ba daidai ba; suna tafiya a hanyoyinsa.

  19. I, Ubangiji, cikin tafiya a hanyar dokokinka, muna sa zuciya gare ka; sunanka da tunani a kanka su ne marmarin zukatanmu.

  20. Raina yana marmarinka da dare; da safe kuma raina yana son ganinka. Sa’ad da hukunce-hukuncenka suka sauko duniya, mutanen duniya kan koyi adalci.

  21. Za a san da zuriyarsu a cikin al’ummai ’ya’yansu kuma a cikin mutane. Dukan waɗanda suka gan su za su san cewa su mutane ne da Ubangiji ya sa wa albarka.”

  22. Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji; raina yana farin ciki a cikin Allahna. Gama ya suturce ni da rigunan ceto ya yi mini ado da rigar adalci, yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja.

  23. Gama kamar yadda ƙasa takan sa tsire-tsire su tohu lambu kuma ya sa iri ya yi girma, haka Ubangiji Mai Iko Duka zai sa adalci da yabo su tsiro a gaban dukan al’ummai.

  24. A ranan nan za a rubuta TSARKI GA Ubangiji a jikin ƙararrawar dawakai, kuma tukwanen dahuwa a gidan Ubangiji za su zama kamar kwanoni masu tsarki a gaban bagade.

  25. Kowace tukunya a Urushalima da Yahuda za tă zama mai tsarki ga Ubangiji Maɗaukaki, kuma duk wanda ya zo don miƙa hadaya zai ɗauki waɗansu tukwane yă yi dahuwa da su. A ranan nan kuwa, ba Bakan’ane da zai ƙara kasance a gidan Ubangiji Maɗaukaki.