Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Famine: Want of seasonable rain
Ayoyi game da Want of seasonable rain
Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya game da fări cewa,
“Yahuda tana makoki biranenta suna fama; suna kuka saboda ƙasar, kuka kuma tana tasowa daga Urushalima.
Manyan mutane suna aika bayinsu su ɗebo ruwa a maɓulɓulai amma babu ruwa. Suka dawo da tulunansu haka nan; da kunya da kuma ƙasƙanci, da kawunansu a rufe.
Ƙasa ta tsattsage saboda babu ruwan sama a ƙasar; manoma sun sha kunya suka kuma rufe kawunansu.