Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Dissension

8 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Ina roƙonku ’yan’uwa, a cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, dukanku ku yarda da juna, domin kada a sami tsattsaguwa a cikinku, domin kuma ku zama ɗaya, cikakku a cikin halinku da tunaninku.

  2. ’Yan’uwana, waɗansu daga iyalin gidan Kulos sun gaya mini cewa, akwai faɗa a cikinku.

  3. Abin da nake nufi shi ne, ɗaya daga cikinku na cewa, “Ni ina bin Bulus,” wani na cewa, “Ni ina bin Afollos,” wani kuma, “Ni ina bin Kefas,” har wa yau wani kuma, “Ni ina bin Kiristi.”

  4. Kiristi a rabe ne? Bulus ne aka gicciye dominku? An yi muku baftisma a cikin sunan Bulus ne?

  5. Har yanzu kuna rayuwa bisa ga halin mutuntaka. Da yake akwai kishi da faɗace-faɗace a cikinku, ba rayuwa irin ta halin mutuntaka ke nan kuke yi ba? Kuma ba rayuwa irin ta mutane ce kawai kuke yi ba?

  6. Gama sa’ad da wani ya ce, “Ni na Bulus ne,” wani kuma ya ce, “Ni na Afollos ne,” ba rayuwa irin ta mutane ke nan kuke yi ba?

  7. Da farko dai, na ji cewa sa’ad da kuka taru a matsayin ikkilisiya, akwai tsattsaguwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen.

  8. Ba shakka dole a sami bambanci a tsakaninku don a nuna wa Allah ya amince da shi a cikinku.