Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Deacon

12 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. A waɗannan kwanaki, sa’ad da yawan almajirai suke ƙaruwa, sai Yahudawan masu jin Hellenanci a cikinsu suka yi gunaguni a kan Yahudawan da suke Ibraniyawa domin ba a kula da gwaurayensu a wajen raba abinci na yau da kullum.

  2. Saboda haka Sha Biyun nan suka tara dukan almajirai wuri ɗaya, suka ce, “Bai zai yi kyau mu bar hidimar maganar Allah don mu shiga hidimar abinci ba.

  3. ’Yan’uwa, ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku waɗanda aka sani suna cike da Ruhu da kuma hikima. Mu kuwa za mu danƙa musu wannan aiki

  4. mu kuwa mu mai da halinmu ga yin addu’a da kuma hidimar maganar Allah.”

  5. Wannan shawarar kuwa ta gamshi dukan ƙungiyar. Sai suka zaɓi Istifanus, mutumin da yake cike da bangaskiya da kuma Ruhu Mai Tsarki; da Filibus, Burokorus, Nikano, Timon, Farmenas, da Nikolas daga Antiyok, wanda ya tuba zuwa Yahudanci.

  6. Suka gabatar da waɗannan mutane wa manzanni, waɗanda kuwa suka yi addu’a, suka ɗibiya hannuwansu a kansu.

  7. Haka masu hidima a cikin ikkilisiya; su ma, su zama maza da sun cancanci girmamawa, masu gaskiya, ba masu yawan shan ruwan inabi ba, ba masu kwaɗayin ƙazamar riba ba.

  8. Dole su riƙe asirin bangaskiya su kuma kasance da lamiri mai tsabta.

  9. Dole a fara gwada su tukuna; sa’an nan in ba a sami wani abin zargi game da su ba, sai su shiga aikin masu hidima.

  10. A haka kuma, dole matansu su zama matan da suka cancanci girmamawa, ba masu gulma ba, sai dai masu sauƙinkai da kuma masu aminci a cikin kome.

  11. Dole mai hidimar ikkilisiya yă zama mijin mace guda dole kuma yă iya tafiyar da ’ya’yansa da kuma iyalinsa da kyau.

  12. Waɗanda suke hidima da kyau suna samar wa kansu kyakkyawan suna da kuma cikakken tabbatarwa a cikin bangaskiyarsu cikin Kiristi Yesu.