Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Cloud

40 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da firistoci suka janye daga Wuri Mai Tsarki, sai girgije ya cika haikalin Ubangiji.

  2. Firistocin kuwa ba su iya yin hidimarsu ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika haikalinsa.

  3. Sa’ad da Solomon ya gama yin addu’a, sai wuta ya sauko daga sama ya cinye hadaya ta ƙonawa da kuma sadakokin, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika haikalin.

  4. Firistoci ba su iya shiga haikalin Ubangiji ba domin ɗaukakar Ubangiji ta cika shi.

  5. Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ga wutar na saukowa, ɗaukakar Ubangiji kuma tana a bisa haikalin, sai suka durƙusa a dakali da fuskokinsu a ƙasa, suka yi sujada suka kuma yi godiya ga Ubangiji suna cewa, “Ubangiji mai alheri ne, ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”

  6. Kerubobin kuwa suna tsaye a gefen kudu na haikali sa’ad da mutumin ya shiga, sai girgije ya cika filin da yake can ciki.

  7. Sai ɗaukakar Ubangiji ya tashi daga bisa kerubobi ya tafi zuwa madogarar ƙofar haikali. Girgijen ya cika haikali, filin kuwa ya cika da hasken ɗaukakar Ubangiji.

  8. Sai ɗaukakar Ubangiji ya tashi daga bisa madogarar ƙofar haikali ya kuma tsaya a bisa kerubobi.

  9. Yayinda nake duba, kerubobin suka buɗe fikafikansu suka kuma tashi daga ƙasa, yayinda suka tafi kuwa, da’irorin suka tafi tare da su. Suka tsaya a mashigin ƙofar gabas na gidan Ubangiji, ɗaukakar Allah na Isra’ila kuwa yana a kansu.

  10. Sa’an nan kerubobi, tare da da’irori kusa da su, suka buɗe fikafikansu, ɗaukakar Allah kuwa tana a bisansu.

  11. Ɗaukakar Ubangiji ta haura daga cikin birnin ta sauka a bisa dutse gabas da shi.

  12. Akwai makiyaya masu zama a fili kusa da wurin, suna tsaron garkunan tumakinsu da dare.

  13. Sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, suka kuwa tsorata ƙwarai.

  14. Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije ya bayyana ya rufe su, sai suka ji tsoro, yayinda suke shiga cikin girgijen.

  15. Wata murya ta fito daga cikin girgijen, tana cewa, “Wannan Ɗana ne, zaɓaɓɓena, ku saurare shi.”