Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Capernaum

88 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ka tafi. Ɗanka zai rayu.” Mutumin kuwa ya amince da maganar da Yesu ya yi ya kuwa tafi.

  2. Tun yana kan hanya, bayinsa suka tarye shi da labari cewa yaron yana warkewa.

  3. Da ya tambayi lokacin da ɗansa ya sami sauƙi, sai suka ce masa, “Zazzaɓin ya sake shi jiya a sa’a ta bakwai.”

  4. Sai mahaifin ya gane a daidai wannan lokaci ne Yesu ya ce masa, “Ɗanka zai rayu.” Saboda haka shi da dukan iyalinsa suka gaskata.

  5. inda suka shiga jirgin ruwa suka tasar wa haye tafkin zuwa Kafarnahum. A lokacin kuwa duhu ya yi, Yesu kuma bai riga ya zo wurinsu ba tukuna.

  6. Iska mai ƙarfi kuwa tana bugowa, ruwaye kuma suka fara hauka.

  7. Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko uku da rabi, sai suka ga Yesu ya kusato jirgin ruwan, yana takawa a kan ruwan; sai suka tsorata.

  8. Amma ya ce musu, “Ni ne; kada ku ji tsoro.”

  9. Sa’an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin ruwan, nan da nan kuwa jirgin ya kai gaɓar da za su.

  10. Kashegari taron da suka tsaya a wancan ƙetaren tafkin suka lura cewa jirgin ruwa ɗaya ne yake a can dā ma, kuma sun lura cewa Yesu bai shiga ciki tare da almajiransa ba, gama sun tashi su kaɗai.

  11. Sai ga waɗansu jiragen ruwa daga Tibariya suka iso kusa da wurin da mutanen suka ci burodi bayan Ubangiji ya yi godiya.

  12. Da taron suka lura cewa Yesu da almajiransa ba sa can, sai suka shiga jiragen ruwa suka tafi Kafarnahum neman Yesu.

  13. Da suka same shi a wancan ƙetaren tafkin, sai suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, yaushe ka kai nan?”