Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Caiaphas

30 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai suka sāke kiransu ciki suka kuma umarce su kada su kuskura su yi magana ko su ƙara koyarwa a cikin sunan Yesu.

  2. Amma Bitrus da Yohanna suka amsa, “Ku shari’anta da kanku ko daidai ne a gaban Allah mu yi muku biyayya maimakon Allah.

  3. Gama ba za mu iya daina yin magana game da abin da muka gani muka kuma ji ba.”

  4. Bayan ƙarin barazana sai suka bar su su tafi. Ba su iya yanke shawara yadda za a hore su ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru.

  5. Gama mutumin da ya sami warkarwar banmamaki, shekarunsa sun fi arba’in.