Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Body

36 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. akan shuka shi da jiki na mutuntaka, a kuma tā da shi da jikin ruhaniya. In akwai jiki na mutuntaka, to, lalle akwai jikin ruhaniya ma.

  2. Haka yake a rubuce cewa, “Adamu, mutumin farko ya zama mai rai”; Adamu na ƙarshe kuwa ruhu ne mai ba da rai.

  3. Ba jikin ruhaniya ne ya zo da farko ba, na mutuntakan ne, daga baya kuma sai na ruhaniya.

  4. Mutumin farko daga turɓaya ce ya fito, mutum na biyu kuwa daga sama ne ya fito.

  5. Kamar yadda mutumin turɓaya yake, haka ma waɗanda suke na turɓaya. Kuma kamar yadda mutumin sama yake, haka ma waɗanda suke na sama.

  6. Kamar dai yadda muka ɗauki siffar mutumin turɓaya, haka kuma za mu ɗauki siffar mutumin sama.

  7. Ina sanar da ku, ’yan’uwa, cewa nama da jini ba za su gāji mulkin Allah ba, haka ma ruɓa ba zai gāji rashin ruɓa ba.

  8. Ku saurara, in gaya muku wani asiri. Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, sai dai duk za a sauya kamanninmu

  9. farat ɗaya, cikin ƙyaftawar ido, da busan ƙaho na ƙarshe. Gama za a busa ƙaho, za a tā da matattu da jiki irin da ba ya ruɓewa, za a kuma sauya kamanninmu.

  10. Gama dole mai ruɓa yă maye wa mai ruɓan nan, marar mutuwa kuma yă maye wa mai mutuwan nan.

  11. Sa’ad da mai ruɓan nan ya maye marar ruɓan nan, mai mutuwa kuma ya maye marar mutuwan nan, sa’an nan ne karin maganar da yake a rubuce zai zama gaskiya cewa, “An haɗiye mutuwa cikin nasara.”