Tsallake zuwa abun ciki

Jehoiakim

37 ayoyi · 7 'yan gida

An kuma san shi da: Eliakim

Ayoyin da suka ambaci Jehoiakim

Tace bisa littafi
  1. A shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji cewa,

  2. A watan tara na shekara ta biyar ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, an yi shela a yi azumi a gaban Ubangiji ga dukan mutanen Urushalima da waɗanda suka zo daga garuruwan Yahuda.

  3. “Ka ɗauki wani littafi ka rubuta a kansa dukan maganar da littafi na farin ya ƙunsa, wanda Yehohiyakim sarkin Yahuda ya ƙone.

  4. Ka kuma faɗa wa Yehohiyakim sarkin Yahuda cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka ƙone wancan littafin ka kuma ce, “Don me ka rubuta a cikinsa, cewa lalle sarkin Babilon zai zo ya hallaka wannan ƙasa, zai kashe mutum duk da dabba?”

  5. Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim sarkin Yahuda. Ba zai kasance da wani wanda zai zauna a kan gadon sarautar Dawuda ba; za a jefar da gawarsa ta sha zafi da rana da dare kuma ta sha matsanancin sanyi.

  6. Sai Irmiya ta ɗauko wani littafi ya ba wa Baruk ɗan Neriya marubuci, kuma yayinda Irmiya yake shibtawa, Baruk ya rubuta a littafin dukan maganar da take a littafin da Yehohiyakim sarkin Yahuda ya ƙone. Ya kuma ƙara ire-iren maganganun nan a kansu.

  7. Nebukadnezzar sarkin Babilon ya naɗa Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda; ya yi mulki a madadin Yehohiyacin ɗan Yehohiyakim.

  8. Ga abin da Irmiya annabi ya faɗa wa Baruk ɗan Neriya a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, bayan Baruk ya rubuta maganar da Irmiya ya shibta masa a kan littafi cewa,

  9. Game da Masar. Ga saƙo game da sojojin Fir’auna Neko sarkin Masar, wanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ci da yaƙi a Karkemish a Kogin Yuferites a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda.

  10. Sarki Zedekiya ya aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda Sarki Yehohiyakim ya yi.

  11. A Shekara ta uku ta mulki Yehohiyakim sarkin Yahuda, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya zo Urushalima ya kuma yi mata ƙawanya.

  12. Sai Ubangiji ya bashe Yehohiyakim sarkin Yahuda a hannunsa, tare da waɗansu kayayyakin haikalin Allah. Ya ɗauki waɗannan kayan zuwa cikin haikalin allahnsa a Babilon cikin ma’ajin gidan allahnsa.