- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Zabura49
Listen to this chapter
0:00
0:00
Kira ga kowa ya ji hikima
1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ku ji wannan, dukanku mutane; ku saurara, dukanku waɗanda suke zama a wannan duniya,
2
babba da yaro mai arziki da talaka.
3
Bakina zai yi maganar hikima; magana daga zuciyata za tă ba da ganewa.
4
Zan juye kunnena ga karin magana; da garaya zan ƙarfafa kacici-kacicina.
Wautar dogara ga dukiya
5
Don me zan ji tsoro sa’ad da mugayen kwanaki suka zo, sa’ad da mugaye masu ruɗu suka kewaye ni,
6
waɗanda suka dogara ga arzikinsu suna kuma fariya a kan yawan arzikinsu?
7
Ba wani da zai iya ceton ran wani ko yă ba wa Allah kuɗin fansa saboda shi,
8
kuɗin fansa domin rai yana da tsada, babu abin da za a biya da ya taɓa isa,
9
da zai sa yă ci gaba da rayuwa har abada yă hana shi shigan kabari yă ruɓa.
10
Gama kowa na iya ganin masu hikima na mutuwa; wawaye da marasa azanci su ma kan hallaka su bar wa waɗansu arzikinsu.
11
Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada, Can za su kasance har zamanai marasa ƙarewa, ko da yake sun ba wa filaye sunayen kansu.
12
Amma mutum, kome arzikinsa, ba ya dawwama; shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.
Kabari yana jiran wawan mai arziki
13
Wannan ne ƙaddarar waɗanda suke dogara a kansu, da kuma ta mabiyansu, waɗanda suka tabbatar da faɗinsu. Sela
14
Kamar tumaki an ƙaddara su ga kabari; za su kuwa zama abincin mutuwa amma masu gaskiya za su yi mulki a kansu da safe. Kamanninsu za su ruɓe a cikin kabari, nesa da gidajensu masu tsada.
15
Amma Allah zai ceci raina daga kabari; tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa. Sela
Kada ku yi kishin nasarar duniya
16
Kada ka razana da yawa sa’ad da mutum ya yi arziki sa’ad da darajar gidansa ta ƙaru;
17
gama ba zai ɗauki kome tare da shi sa’ad da ya mutu ba, darajarsa ba za tă gangara tare da shi ba.
18
Ko da yake yayinda yake a raye ya ɗauka kansa mai albarka ne, mutane kuma sun yabe ka sa’ad da kake cin nasara,
19
zai gamu da tsarar kakanninsa, waɗanda ba za su taɓa ganin hasken rayuwa ba.
20
Mutumin da yake da arziki ba tare da ganewa ba shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.
Use ← → arrow keys to navigate
Settings
Reading Style
Typeface
Font Size px
Reading Width chars
Options
Study Note