Skip to content
Waƙar Waƙoƙi 2:1-7

Waƙar Waƙoƙi 2:1-7

1
Ni furen bi-rana ne na Sharon, furen bi-rana na kwari.
2
Kamar furen bi-rana a cikin ƙayayyuwa haka ƙaunatacciyata take a cikin ’yan mata.
3
Kamar itacen gawasa a cikin itatuwan jeji haka ƙaunataccena yake a cikin samari. Ina farin ciki in zauna a inuwarsa, ’ya’yan itacensa suna da daɗin ɗanɗanon da nake so
4
Ya kai ni babban zauren da ake liyafa, ƙauna ita ce tutarsa a gare ni.
5
Ka ƙarfafa ni da zabibi ka wartsake ni da gawasa, gama ina suma don ƙauna.
6
Hannunsa na hagu yana a ƙarƙashin kaina, hannunsa na dama kuma ya rungume ni.
7
’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari da bareyi da ƙishimai na jeji. Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba sai haka ya zama lalle.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options