Skip to content
Romawa 16:5-12

Romawa 16:5-12

5
Ku kuma gai da ikkilisiyar da take haɗuwa a gidansu. Ku gai da ƙaunataccen abokina Efenetus, wanda ya zama na farko a karɓar Kiristi a lardin Asiya.
6
Ku gai da Maryamu wadda ta yi muku aiki tuƙuru.
7
Ku gai da Anduronikus da Yuniyas, dangina waɗanda aka daure a kurkuku tare da ni. Su fitattu ne sosai a cikin manzanni, sun riga ni zama masu bin Kiristi.
8
Ku gai da Amfiliyatus, ƙaunataccena a cikin Ubangiji.
9
Ku gai da Urbanus, abokin aikinmu cikin Kiristi, da kuma ƙaunataccen abokina Sitakis.
10
Ku gai da Afelles wanda amincinsa cikin Kiristi tabbatacce ne. Ku gai da iyalin gidan Aristobulus.
11
Ku gai da ɗan’uwana, Hirodiyon. Ku gai da iyalin gidan Narkissus da suke cikin Ubangiji.
12
Ku gai da Tiryifena da Tiryifosa, matan nan da suke aiki tuƙuru cikin Ubangiji. Ku gai da ƙaunatacciyata Fersis, wata matan da ta yi aiki tuƙuru cikin Ubangiji.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options