1
Ina gabatar muku da ’yar’uwarmu Fibi, baranyar ikkilisiya a Kenkireya.
2
Ina roƙonku ku karɓe ta a cikin Ubangiji yadda ya dace a karɓi tsarkaka a kuma ba ta kowane irin taimakon da take bukata daga wurinku, gama ta zama mai taimako ƙwarai ga mutane masu yawa, haɗe da ni ma.