Ƙidaya 22:34-39
34
Bala’am ya ce wa mala’ikan Ubangiji, “Na yi zunubi. Ban san ka tsaya a hanya don ka hana ni ba. Yanzu in ba ka ji daɗin tafiyata, sai in koma.”
35
Mala’ikan Ubangiji ya ce wa Bala’am, “Ka tafi tare da mutanen, amma abin da na faɗa maka ne kaɗai za ka faɗa.” Saboda haka Bala’am ya tafi tare da dattawan Balak.
36
Da Balak ya ji cewa Bala’am yana zuwa, sai ya fito, ya tarye shi a garin Mowabawa da suke a iyakar Arnon, a ƙarshen yankinsa.
37
Balak ya ce wa Bala’am, “Ban aika maka saƙo cikin gagawa ba? Me ya sa ba ka zo ba? Ko ban isa in sāka maka ba ne?”
38
Bala’am ya amsa ya ce, “To, ai, ga shi, na zo yanzu. Ina da wani ikon yin wata magana ne? Dole in faɗa abin da Allah ya ce in faɗa ne kawai.”
39
Sa’an nan Bala’am ya tafi tare da Balak zuwa Kiriyat-Huzot,
Settings