Ƙidaya 23:1-6
1
Bala’am ya ce, “Ka gina mini bagadai bakwai a nan, ka shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.”
2
Balak ya yi yadda Bala’am ya faɗa, sai su biyu suka miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.
3
Sa’an nan Bala’am ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka, ni kuwa in koma wani wurin da yake a kaɗaice. Wataƙila Ubangiji zai sadu da ni. Duk abin da ya bayyana mini, zan faɗa maka.” Sai ya haura kan wani wurin da yake a kaɗaice a tudun.
4
Allah kuwa ya sadu da Bala’am. Bala’am ya ce, “Na shirya bagadai bakwai, na kuma miƙa bijimi guda da rago guda, a kan kowane bagade.”
5
Ubangiji ya ba wa Bala’am saƙo ya ce, “Ka koma wurin Balak, ka faɗa masa wannan saƙo.”
6
Saboda haka, sai Bala’am ya koma wurin Balak ya same shi tsaye a kusa da hadayarsa, tare da dukan dattawan Mowab.
Settings