Skip to content
Ƙidaya 11:18-34

Ƙidaya 11:18-34

18
“Ka gaya wa mutane, ‘Ku tsarkake kanku don gobe, za ku ci nama. Ubangiji ya ji ku sa’ad da kuka yi kuka cewa, “Da mun sami nama mun ci mana! Ai, da ba mu da damuwa, gama lokacin da muke zama cikin Masar ba mu da damuwa!” Yanzu Ubangiji zai ba ku nama, za ku kuma ci.
19
Ba za ku ci shi na kwana ɗaya, ko biyu, ko biyar, ko goma, ko kuma kwana ashirin kaɗai ba,
20
amma za ku ci har na wata guda cur, sai ya gundure ku a hanci har ku yi ƙyamarsa, domin kun ƙi Ubangiji wanda yake cikinku, kuka yi kuka a gabansa, kuna cewa, “Don me ma muka bar ƙasar Masar?” ’ ”
21
Amma Musa ya ce, “Ga ni a cikin mutane dubu ɗari shida tafe tare da ni, kana kuma cewa, ‘Zan ba su nama su ci har wata guda cur!’
22
Za su ma sami isashe in har aka yanka musu garkuna tumaki da na shanu? Za su sami isashe in aka kama musu dukan kifin teku?”
23
Ubangiji ya ce wa Musa, “Akwai abin da ya fi ƙarfina ne? Bari ka gani ko abin da na ce zan yi, zai faru ko babu.”
24
Saboda haka Musa ya fita ya gaya wa jama’a abin da Ubangiji ya faɗa. Ya tattaro dattawansu saba’in, ya sa suka tsaya kewaye da Tentin Sujada.
25
Sa’an nan Ubangiji ya sauko daga girgije, ya yi magana da shi, ya kuma ɗauke Ruhun da yake kan Musa ya ɗora shi a kan dattawa saba’in nan. Sa’ad da Ruhun ya zauna a kansu, sai suka yi annabci, amma daga wannan ba su ƙara yin haka kuma ba.
26
To, fa, akwai dattawa biyu da suka kasance a sansani, wato, Eldad da Medad. Su ma an lasafta su cikin dattawan, amma ba su fita zuwa Tentin Sujada ba. Duk da haka Ruhun ya sauka a kansu, suka kuma yi annabci a cikin sansanin.
27
Wani saurayi ya sheƙa a guje zuwa wajen Musa ya ce, “Eldad da Medad suna can suna annabci a sansani.”
28
Sai Yoshuwa ɗan Nun, wanda yake mataimakin Musa tun yana saurayi, ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, Musa, ka hana su!”
29
Amma Musa ya amsa ya ce, “Kana kishi domina ne? Da ma a ce dukan mutanen Ubangiji annabawa ne, da ma a kuma ce Ubangiji ya sa Ruhunsa a kansu mana!”
30
Sai Musa da dattawan Isra’ila suka koma sansani.
31
Ana nan, sai Ubangiji ya kawo wata iska mai tsanani ta koro makware daga teku. Ta bar su birjik kewaye da sansani, tsayinsu daga ƙasa ya kai kamu biyu, misalin tafiyar nisan yini guda ta kowace fuska.
32
Dukan yini da dukan dare da kuma kashegari, mutane suka fito suka tattara makware. Ba wanda ya kāsa tara ƙasa da garwa goma. Sai suka shanya abinsu kewaye da sansanin.
33
Amma da suna cikin cin naman, tun ba su ma haɗiye ba, sai Ubangiji ya husata sosai a kan jama’ar, ya buge su da annoba mai zafi.
34
Saboda haka aka kira wannan wuri Kibrot Hatta’awa, gama a can ne aka binne mutanen nan makwaɗaita.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options