Skip to content
Nehemiya 7:5-64

Nehemiya 7:5-64

5
Sai Allahna ya sa a zuciyata in tara manyan gari, shugabanni da talakawa don a rubuta su bisa ga iyalansu. Na sami littafin asali na waɗanda suka fara dawowa. Ga abin da na tarar an rubuta a ciki.
6
Waɗannan su ne mutanen yankin da suka dawo daga zaman bautar da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kame (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowanne zuwa garinsa.
7
Sun dawo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Azariya, da Ra’amiya, da Nahamani, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Nehum da kuma Ba’ana). Ga jerin mutanen Isra’ila.
8
Zuriyar Farosh mutum 2,172
9
ta Shefatiya 372
10
ta Ara 652
11
ta Fahat-Mowab (ta wurin Yeshuwa da Yowab) 2,818
12
ta Elam 1,254
13
ta Zattu 845
14
ta Zakkai 760
15
ta Binnuyi 648
16
ta Bebai 628
17
ta Azgad 2,322
18
ta Adonikam 667
19
ta Bigwai 2,067
20
ta Adin 655
21
ta Ater (ta wurin Hezekiya) 98
22
ta Hashum 328
23
ta Bezai 324
24
ta Harif 112
25
ta Gibeyon 95.
26
Mutanen Betlehem da na Netofa 188
27
na Anatot 128
28
na Bet-Azmawet 42
29
na Kiriyat Yeyarim, Kefira da na Beyerot 743
30
na Rama da na Geba 621
31
na Mikmash 122
32
na Betel da na Ai 123
33
na ɗayan Nebo 52
34
na ɗayan Elam 1,254
35
na Harim 2 320
36
na Yeriko 345
37
na Lod, da na Hadid, da na Ono 721
38
na Sena’a 3,930.
39
Ga zuriyar Firistoci. Zuriyar Yedahiya (ta wurin iyalin Yeshuwa) 973
40
ta Immer 1,052
41
ta Fashhur 1,247
42
ta Harim 1,017.
43
Ga zuriyar Lawiyawa. Zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel (ta wurin Hodeba) 74.
44
Mawaƙa. Zuriyar Asaf mutum 148.
45
Ga zuriyar Matsaran Ƙofofi. Zuriyar Shallum, Ater, Talmon, Akkub, Hatita da Shobai 138.
46
Ma’aikatan haikali. Zuriyar Ziha, Hasufa, Tabbawot,
47
da ta Keros, da ta Siya, da ta Fadon,
48
da ta Lebana, da ta Hagaba, da ta Shalmai,
49
da ta Hanan, da ta Giddel, da ta Gahar,
50
da ta Reyahiya, da ta Rezin, da ta Nekoda,
51
da ta Gazzam, da ta Uzza, da ta Faseya,
52
da ta Besai, da ta Meyunawa, da ta Nefussiyawa,
53
da ta Bakbuk, da ta Hakufa, da ta Harhur,
54
da ta Bazlit, da ta Mehida, da ta Harsha,
55
da ta Barkos, da ta Sisera, da ta Tema,
56
da ta Neziya, da kuma ta Hatifa.
57
Ga zuriyar bayin Solomon. Zuriyar Sotai, da ta Soferet, da ta Ferida,
58
da ta Ya’ala, da ta Darkon, da ta Giddel,
59
Shefatiya, Hattil, Fokeret-Hazzebayim, da Amon.
60
Zuriyar ma’aikatan haikali da ta bayin Solomon su 392.
61
Waɗansu sun hauro daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addon da Immer, amma ba su iya nuna cewa iyalansu su zuriyar Isra’ila ce ba,
62
zuriyar Delahiya, Tobiya, da Nekoda 642.
63
Na wajen firistoci kuwa su ne, Zuriyar Hobahiya, da ta Hakkoz, da ta Barzillai (wani mutumin da ya auri ’yar Barzillai mutumin Gileyad, aka kuma kira shi da wannan suna).
64
Waɗannan ne aka nemi sunayensu a cikin tarihin asalin iyalai, amma ba a same su a ciki ba, saboda haka aka hana su shiga cikin firistoci, sun zama kamar marasa tsarki.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options