Skip to content
Mika 1:1-9

Mika 1:1-9

1
Maganar Ubangiji ta zo wa Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da kuma na Hezekiya, sarakunan Yahuda, Mika ya ga wahayi a kan Samariya da kuma a kan Urushalima. Ga abin da ya ce.
2
Ku ji, ya ku mutane duka, ki saurara, ya ke duniya da dukan mazauna cikinki, bari Ubangiji Mai Iko Duka yă zama shaida a kanku, daga haikalinsa mai tsarki.
3
Duba! Ubangiji yana zuwa daga wurin zamansa; zai sauko yă taka maɗaukakan wuraren duniya.
4
Duwatsu za su narke a ƙarƙashin ƙafafunsa, kamar kaki a gaban wuta, kwaruruka kuma za su ɓace, kamar ruwan da yake gangarowa daga tsauni.
5
Duk wannan zai faru saboda laifin Yaƙub, da kuma zunuban gidan Isra’ila ne. Mene ne laifin Yaƙub? Shin, ba Samariya ba ce? Ina ne maɗaukakan wuraren Yahuda? Shin, ba Urushalima ba ce?
6
“Saboda haka zan mai da Samariya tarin juji, wurin noman inabi. Zan zubar da duwatsunta a cikin kwari in kuma bar harsashin gininta a bayyane.
7
Za a ragargaje dukan allolinta; za a ƙone dukan baye-bayenta na haikali da wuta; zan lalatar da dukan gumakanta. Tun da ta wurin karuwanci ne ta tattara su, ga karuwanci kuma za su koma.”
8
Saboda wannan zan yi baƙin ciki, in yi kuka; zan yi tafiya ba takalmi, zan tuɓe, in kuma yi tafiya tsirara. Zan yi kuka kamar dila, in yi baƙin ciki kamar mujiya.
9
Gama raunin Samariya ba mai warkewa ba ne; ya bazu har Yahuda. Ya ma kai bakin ƙofar mutanena, har ma Urushalima da kanta.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options